Za a binciki hadarin jirgin Pakistan

Karikicen jirgin da ya yi hadari a Pakistan Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Karikicen jirgin da ya yi hadari a Pakistan

Gwamnatin Pakistan ta umurci a gudanar da bincike akan hadarin jirgin saman da aka yi a ranar Juma'a a kasar.

An yi hadarin ne a kusa Islamabad babban birnin kasar.

Mutane dari da ashirin da bakwai ne suka mutu a hadarin.

Jami'ai sun ce an gano dukkan gawarwakin dake cikin jirgin.

An haramtawa mai kamfanin jirgin da ya yi hadarin barin kasar.

irgin, wanda ya taso daga Karachi, ya fada cikin mawuyacin hali ne 'yan mintuna kadan kafin ya sauka.

Kamfanin da ya mallaki jirgin, Bhoja, ya ce rashin kyawun yanayi ne ya haddasa hadarin.

An dai yi ruwa da iska tare da tsawa mai karfin gaske a yankin a lokacin.

Ana ma tsokacin cewa walkiya ce ta bugi jirgin.