An sako likitan Spain da aka sace a Najeriya

Rahotanni daga Najeriya, sun ce an sako likitan nan dan kasar Spain Dokta Joe Machimbarrena da aka sace a kasar a farkon wannan watan.

An sace likitan ne a birnin Enugu, inda yake aiki a wani asibiti.

An ce an sami likitan ne a wani wajen na birnin, kuma yana cikin koshin lafiya.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Enugu, Mista Ebere Amaraizu, ya ce a daren jiya ne aka yi aune da liktan ne a wata Unguwa da ake kira Thinkers' Corner da ke birnin Enugun.

Har yanzu dai babu karin bayani game da batun sakin likitan; watau walau sai da aka biya fansar kudi kafin a sako shi ko kuma ba a biya ko da kwandala ba.

Sai dai an bayar da tabbaci cewa, yana cikin koshin lafiya, ko da yake yana tattare da gajiya, kuma bai kai ga furta wasu bayanai ba tukun. Tun ran hudu ga wannan wata na Afrilu ne ake zargin wasu mutane da ba a kai ga sanin ko su wane ne ba, suka sace shi liktan dan kasar Spain daga gidansa a nan birnin Enugu, kuma suka yi garkuwa da shi. Likitan mai shekaru hamsin da takwas a duniya, yanza aiki ne da wani asibiti mai zaman kansa, wanda wata kungiyar cocin darikar Katolica take tallafa wad a kudi. Sace mutane a yi garkuwa da su wata gagarumar matsala ce da ta rutsa da mutane da dama a Najeriya, musamman ma a yankin Naija-Delta.