Za a tura masu sa ido Syria

Hakkin mallakar hoto AP

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri'ar tura tawagar masu sa ido ta sojojin da basa dauke da makamai kimanin dari ukku zuwa Syria.

Tawagar zata kwashe watanni uku tana sa ido kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta tare da taimakawa wajen aiwatar da shirin samar da zaman lafiya da gwamnatin Syrian tai na'am da shi.

Baki yazu daya a kwamatin kan tura tawagar, duk kuwa da fargabar da kasashen yammaci ke yi na gazawar Syria na tabbatar da yarjejeniyar.

Bashar Jafari, jakadan Syria a Majalisar Dinkin Duniya ya ce: "muna son mu ja hankalin masu sa idon cewa tilasne su yi aikinsu kan ba sani ba sabo da kuma kwarewa."

Sai da daka yi ta mahawara kafun a amince da kudirin.

Kasahen Turai sun ce kada a tura masu sa idon da basu dauke da makamai har sai Syria ta janye dakarunta da tankokin yaki.

Rasha da ake yiwa kallon kawa ce ga Syriayar tace yakamata a tura masu sa idon cikin gaggawa.

A karshe dai yarjejeniyar ta baiwa Ban Kimoon, Sakatare Janar na MMD damar yanke shawara akan yadda za a tura masu sa idon da kuma lokacinda za tura su

Karin bayani