Ana zaben shugaban kasa na Faransa

Hakkin mallakar hoto AFP

Ana gudanar da zaben shugaban Kasar Faransa zagaye na farko inda za a fafata tsakanin yan takara goma da suka tsaya a zaben.

Dokokin zaben Kasar dai sun haramtawa 'yan takara gudanar da kamfe da kuma jin ra'ayoyin jama'a a ranar zabe.

Shugaba mai ci Nicolas Sarkozy dai yana fuskantar kalubale daga dan-gurguzu Francois Hollande, da kuma wasu 'yan takara guda takwas.

Ana ganin ba makawa sai an kai zagaye na biyu a zaben saboda irin kalubalen da Shugaba Sarkozy ke fuskanta

zaben na gudana ne a wani lokaci na rashin tabbas game da tattalin arzikin kasar, kuma ana ganin cewar ba za a sami fitowar jama'a sosai ba a zagayen farko na zaben.

Karin bayani