Sarkozy ya sha kaye a zagayen farko

Hakkin mallakar hoto AFP

An kammala zagayen farko na zaben shugaban kasa a Faransa inda François Hollande na jam'iyyar gurguzu ya kada shugaba mai ci Nicolas Sarkozy.

Hollande ya samu kashi ashirin da takwas ne cikin dari yayinda da kuma Sarkozy ya samu kashi ashirin da biyar cikin dari na kuri'ar da aka kada.

Hakan na nufin 'yan takarar biyu zasu kara a zagaye na biyu na zaben, wanda za a yi a wata mai zuwa.

Duka dai 'yan takara goma ne suka shiga zaben

Karin bayani