Mutane biyu sun mutu a rikicin Libya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Libya

Rahotanni daga kudancin Libya na cewa akalla mutane biyu aka kashe a wani rikici tsakanin dakarun gwamnati da kuma 'yan wata kabila a garin Kufra.

An dai ce anyi amfani da manyan makamai a garin na Kufra dake cikin hamada, inda shugaban kabilar Toubou ya zargi sojoji da amfani da rokoki da kuma bindigogi akan mutanen sa.

Fadan da aka kashe mutane biyu tare da jikkata goma sha biyar na nuni da rikicin cikin gidan da aka jima dashi da kuma yawaitar makamai a hannun farar hula a kasar tun bayan da aka murkushe mulkin marigayi moammar ghaddafi watanni takwas baya.

A watan daya gabata ma dai an sami rikici daya hada da 'ya kabilar Toubou, inda aka kashe mutane akalla saba'in a kudancin Libyan

Karin bayani