Najeriya ta dakatar da kamfanonin da suka binciki kudin tallafi

Hakkin mallakar hoto AFP

Gwamnatin Najeriya ta dakatar da aikin wasu kamfanoni dake gudanar da bincike kan yadda ake biyan kudaden tallafin man fetur.

Wannan ne matakin farko da gwamnatin ta dauka game da badakalar cin hanci da rashawa wurin biyan kudaden tallafin man fetur a kasar wanda majalisar wakilai ke gudanarwa.

Kimanin Naira Trillion daya ne majalisar wakilan Nigeriar ta yi zargin cewa an yi sama da fadi da su, wurin biyan tallafin man fetur.

Kamfanonin dake gudanar da binciken kudaden da aka dakatar su ne Akintola Williams and Co da kuma Adekanola and Co.

A cewar Paul Nwabuiku maitakin ministan kula da harkokin kudin Nigeria Ngozi Okonjo Iweala, ma'aikatar kudin Nigeria ta dauki wannan matakin ne bayanda su ka yi nazari kan binciken da majalisar wakilan Nigeria ta gudanar kan yadda ake kashe kudaden tallafin man fetur.

Ita dai majalisar wakilan Nigeria, ta kammala biciken ta ne kan kudaden tallafin na man fetur inda ta ce, akwai almundahana da cin hanci da rashawa da rashin sanin makamar aiki a harkar tallafin man fetur.

Ma'aikatar kudi ta Nigeriar, ta kafa wani kwamiti wanda zai duba yadda za a maye gurbin kamfanonin da aka dakatar.

To saidai babu wani bayani game da yiwuwar gurfanar da kamfanonin gaban kuliya.