An kada kuri'ar tura soji 300 Syria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption majalisar dinkin duniya

Majalisar dinkin duniya ta kada kuri'ar tura sojoji wadanda basa dauke da makamai su dari uku, wadanda zasu sa ido akan yarjejeniyar tsagaita wuta a Syria

Zasu shafe watanni uku suna sa ido akan yarjejeniyar tsagaita wutar, da kuma taimakawa wajen aiwatar da shirin zaman lafiya da gwamnatin Syrian ta amince da shi.

Tunda farko dai wasu masu- sa- idon 'yan kalilan su isa Syrian tuni, kuma sun kai ziyararsu ta fako zuwa inda 'yan adawa suke da karfi a birnin Homs

Masu fafutuka dai sunce an kashe mutane arba'in a ranar asabar, wadanda suka hada da wasu mutum goma sha- biyar da suka fito daga gida daya a Deraa

Karin bayani