Za a fafata tsakanin Sarkozy da Hollande

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Hollande da Sarkozy

Babban mai kalubalantar zaben shugabancin Kasar Faransa, dan jam'iyyar gurguzu, Francois Hollande, zai fafata da Sarkozy bayanda ya samu nasarar zagayen farko na zaben.

Mr Hollande ya samu kashi 28 da rabi cikin 100 na kuri'un da aka kada a zaben.

Shi kuwa Shugaban Kasar Nicolas Sarkozy na da kashi 27 cikin 100, kaso mafi kankanta a tarihi a matsayin shugaban Kasa mai ci.

Su biyun dai, zasu fafata da juna a zagaye na biyu a wata mai zuwa

Karin bayani