An yi jana'izar tsohon shugaban Malawi

jana'izar tsohon shugaban Malawi
Image caption jana'izar tsohon shugaban Malawi

Dubban 'yan kasar Malawi ne suka yi dafifi a gonar Ndata, wadda makekiyar gona ce da ta kunshi gidajen kwana, ta tsohon shugaban kasar, Bingu wa Mutharika.

Sun je ne domin halartar jana'izarsa.

Ranar biyar ga watan Aprilun nan ne, masanin tattalin arzikin da ya koma harkokin siyasa, ya rasu yana da shekaru saba'in da takwas, a sakamakon bugun zuciya.

Bayan rasuwarsa an yi ta kai ruwa-rana a kokarin nada wanda zai gaje shi, sakamakon sabanin dake tsakaninsa da matimakiyarsa, Joyce Banda.

A baya an ce sai da ta kai ga Marigayi shugaba Mutharika ya kori Joyce Banda daga jam'iyya mai mulki.

A karshe bisa la'akari da tanajin tsarin mulki tilas aka rantsar da Mrs Joyce Banda a matsayin shugabar kasa, kuma zata ci gaba da rike mukamin na tsawon shekaru biyu, kafin gudanar da sabon zabe.

Karin bayani