Sudan da Sudan ta kudu sun gwabza fada

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojin Sudan

Sudan ta Kudu da Sudan sun sake gwabza fada a kan iyakar da suke takaddama a kai. Kasashen biyu dai sun gaza samun masalaha kan iyakoki da rijiyoyin mai.

wani kakakin sojin Sudan ta kudu yace dakarun sojin Sudan sun farma yankin Sudan ta kudu kusan kilomita tara da shiga iyakar Sudan ta kudu din, inda suka yi amfani da tankokin yaki da bindigogin atilare.

Kakakin Sojin Sudan ma ya tabbatar da cewa an gwabza fadan, amma ya musanta cewa sun shiga yankin Sudan ta kudu.

Sudan ta kudu dai, ta samu cin gashin kanta ne daga Sudan a watan Julin shekarar da ta gabata, amma har yanzu basa jituwa akan ikon mai da kuma kan iyakokinsu.

Karin bayani