BBC navigation

Sudan da Sudan ta kudu sun gwabza fada

An sabunta: 23 ga Aprilu, 2012 - An wallafa a 07:53 GMT

Sojin Sudan

Sudan ta Kudu da Sudan sun sake gwabza fada a kan iyakar da suke takaddama a kai.
Kasashen biyu dai sun gaza samun masalaha kan iyakoki da rijiyoyin mai.

wani kakakin sojin Sudan ta kudu yace dakarun sojin Sudan sun farma yankin Sudan ta kudu kusan kilomita tara da shiga iyakar Sudan ta kudu din, inda suka yi amfani da tankokin yaki da bindigogin atilare.

Kakakin Sojin Sudan ma ya tabbatar da cewa an gwabza fadan, amma ya musanta cewa sun shiga yankin Sudan ta kudu.

Sudan ta kudu dai, ta samu cin gashin kanta ne daga Sudan a watan Julin shekarar da ta gabata, amma har yanzu basa jituwa akan ikon mai da kuma kan iyakokinsu.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.