Majlisa ta zargi Cameron da tafka kura-kurai

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption David Cameron

Rahotan wani kwamitin 'yan majalisar dokoki ya zargi Prime Ministan Burtaniya David Cameron da tafka wasu kurakurai.

An dai tilastawa Gwamnatin Burtaniyan data kare kanta a 'yan makonnin nan, game da martanin data mayar, bayan da direbobin tankokin daukar mai sukai barazanar tafiya yajin aiki.

Gami da kuma wasu canje- canje da aka gudanar a alawus- alawus din 'yan fansho da suka janyo cece- kuce, da kuma harajin da aka sanya akan wani na'uin abinci.

A yanzu dai kwamitin yayi gargadin shugabanci mai rauni, ya kuma ce ana kawo dabaru da zasu janyo rikici da kuma raguwar yarda da gwamnati.

Karin bayani