Likitoci na yajin aikin dindindin a Lagos

A Najeriya, likitoci a jihar Lagos sun fara wani yajin aiki na sai abin da hali- ya-yi.

Likitocin na yajin aikin ne domin neman a kyautata masu yanayin aiki.

Ko a makon da ya gabata sai da suka yi wani yajin aikin na gargadi, lamarin da ya sa gwamnatin jihar Lagos din kafa wani kwamitin bincike.

Image caption Yajin aiki a Najeriya

Yayin da likitocin ke adawa da kafa kwamitin, gwamnatin jihar Lagos na cewa wajibi ne ta bi bahasin yajin aikin, da niyyar daukar matakan ladabtarwa kan duk wanda aka samu da laifi.

Karin bayani