Majalisar Najeriya na muhawara kan tallafin mai

Hakkin mallakar hoto b
Image caption wasu yan Najeriya suna shan mai

A Najeriya, majalisar wakilan kasar ta fara tafka muhawara a kan rahoton kwamitinta da ya yi bincike kan kudaden da ake kashewa wurin tallafin man fetur a kasar.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu kamfanoni suka bayyana rashin gamsuwar su da irin abubuwan da rahoton ya kunsa.

Kimanin Naira Triliyan daya ne dai kwamitin yayi zargin cewa an wawure, wurin biyan kudaden tallafin man fetur.

'Yan majalisar sun ce, zasu mika sunan duk wanda ake zargi da aikata ba daidai ba ga Hukumar dake kula da yiwa arzikin kasa ta'annati, wato EFCC, domin ta tuhume shi.

Karin bayani