Yau za a yankewa Charles Taylor hukunci

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Charles Taylor

A ranar Alhamis ne ake sa ran kotun duniya da ke birnin Hague za ta yanke hukunci ga tuhumar da take yi wa tsohon shugaban Liberia, Charles Taylor, tun shekaru hudu da suka wuce.

Ana zargin Mr Taylor da aikata laifukan yaki, da cin zarafin bil-adama bayan ya rura wutar mummunan yakin basasar da aka shafe shekaru goma ana yi a kasar Saliyo cikin shekarun 1990.

Masu gabatar da kara sun zarge shi da laifuka na kisan kai, da fyade da daddatse hannuwa da kafafun mutane da kuma amfani da kananan yara a matsayin sojoji.

An kuma zarge shi da amfana da kasuwanci na lu'u-lu'u a lokacin yakin.

Mr Taylor dai ya musanta laifukkan da ake tuhumar sa da aikatawa, yana mai cewa makirci ne kawai na siyasa aka yi masa.

Ya ce, "wannan wani kamfe ne na batanci da ake yi wa Charles Taylor da gwamnati na; an ci gaba da yi babu kakkautawa".

Karin bayani