An yankewa Firayim Ministan Pakistan hukunci

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Yousuf Raza Gilani

A kasar Pakistan, Kotun Koli ta samu Firayim Minista, Yousuf Raza Gilani, da laifin raina umurnin ta.

An zargi Mr Gilani ne da laifin kin bin umurnin Kotu na rubuta wasika zuwa kasar Switzerland, ya gaya mata ta sake bude kararraki na cin hanci da rashawa da ake yi wa shugaban Pakistan, Asif Ali Zardari.

Sai dai kotun ta zartar wa Mr Gilanin da hukuncin da ba ta fayyace ba, ta kyale shi ya ci gaba da zama kan mukaminsa zuwa wani lokaci.

A yanzu dai ba za a iya tantance wa ba ko wannan hukunci zai sanya a sauke shi daga mukaminsa a nan gaba.

Karin bayani