Pakistan ta gwada sabon makami mai linzami

Pakistan ta gwada sabon makami mai linzami
Image caption Gwajin na Pakistan na zuwa ne kwanaki kadan bayan India ta yi nata

Kasar Pakistan tace ta yi nasarar gwajin makami mai linzami mai matsakaicin zango, wanda kuma zai iya daukar makamin nukiliya.

Pakistan din ta kuma ce, ta harba makamin ne cikin teku da safiyar ranar Laraba, wato mako guda kenan bayan India ita ma ta yi gwajin makamin mai linzami mai cin dogon zango.

Jami'an Sojin Pakistan din basu kayyade adadin nisan da sabon makamin mai linzamin da aka yiwa lakabi da 2,500.

Wani faifen bidiyo da aka watsa ya nuna yadda aka kaddamar da rokar, yayin da kuma manyan jami'an sojin ke sowa suna tafi.

Rundunar Sojin Pakistan ta ce makamin na Shaheen-one-A ya kara karfin tafiya da cin dogon zangon, amma sun kasa kayyade yawan adadin nisan da zai iya kaiwa.

Sun dai ce makamin zai iya yin tasiri wajen harba makaman nukiliya ko kuma na yaki wadanda aka saba harbawa.