"Charles Taylor ya rura wutar rikicin Sierra Leone"

Charles Taylor
Image caption An samu Charles Taylor da laifuka 11 da suka hada da ta'addanci da laifukan yaki

An samu tsohon shugaban Liberia Charles Taylor da laifin taimakawa wurin aikata laifukan yaki a yakin basasar kasar Sierra Leone a shari'ar da ake yi masa a kotun laifukan yaki ta musamman a birnin Hague.

Kotu za ta zauna ranar 16 ga watan Mayu domin duba hukuncin da za a yanke masa, yayin da za a yanke hukuncin a ranar 30 ga watan na Mayun 2012.

Bayanan da muka gabatar muku

13:27: Mun kawo karshen bayanan da muke kawo muku kai tsaye kan shari'ar da ake yi wa tsohon shugaban Liberia Charles Taylor, inda kotu ta same shi da laifin taimakawa da rura wutar aikata laifukan yaki a lokacin yakin basasar da aka tafka a kasar Sierra Leone. Za a yanke masa hukunci a ranar 30 ga watan Mayun 2012.

12:49: A sakon Suleiman Ibrahim taBBC Hausa facebook, ya kamata kotu ta yi masa hunkunci mai tsanani domin zama darasi ga masu mulkin kama karya.

12:47: Kungiyar kare hakkin bil'adama da Amnesty International ta ce hukuncin wani gagarumin sako ne ga shugabannin kasashe. "Yayin da hukuncin na yau ya samar da wani mataki na adalci ga jama'ar Serrie Leone, Mr Taylor da sauran jama'a da za a yanke wa hukunci wata manuniya ce kawai ta tabbatar da adalci," a cewar Brima Abdulai Sheriff na kungiyar a wata sanarwa.

12:33: A takaice alkalin kotun mai shari'a Lussick ya ce an samu Charles Taylor da laifin taimakawa wajen aikata laifuka 11, sai dai ya ce masu gabatar da kara sun kasa tabbatar da cewa yana cikin gungun masu aikata laifuka.

12:18: Kotu ta amince ta dage wannan shari'a zuwa ranar 16 ga watan Mayu domin zaman yanke hukunci a kan Charles Taylor, bayan ta same shi da laifin taimakawa 'yan tawayen RUF a rikicin kasar Sierra Leone. Za kuma a bayyana hukuncin ne a ranar Laraba 30 ga watan Mayun 2012.

12:14: Alkali ya lissafa tuhumce-tuhumce 11, sannan ya nemi Mr Taylor ya zauna

12:11: An nemi Charles Taylor ya mike tsaye domin karanta masa hukuncin kotu

12:09: An ci gaba da shari'ar a Hague. Kotu ta samu Charles Taylor da laifin shirya laifukan yakin da aka aikata a kasar Sierra Leone

12:04: An dakatar da ci gaba da shari'ar zuwa wani dan lokaci saboda alkalin ya ce faifan da ke nadar shari'ar ya cika

11:59: Alkalin kotun Richard Lussick ya ce goyon baya ta fannin soji da wanda ake zargin ya bayar ga 'yan tawayen RUF, ya taimaka matuka-gaya wurin aikata laifukan yaki

11:56: Jama'a sun taru a kotun duniya ta musamman kan rikicin kasar Sierra Leone ciki har da wadanda rikicin ya ritsa da su domin kallon hukuncin da kotun ta ke yanke wa a Hague kai tsaye.

11:52: Kotu ta tabbatar da cewa wanda ake zargin ya taimakawa 'yan tawayen RUF ta fuskoki da dama ciki har da kudade.

11:50: Ishmael Bayoh ta shafin Facebook na BBC Africa cewa yayi: " Ina tare da rediyota ina sauraren wannan hukunci ta BBC. Ina tsakiyar birnin Freetown na Sierra Leone wanda ya fuskanci lugudan wuta a 1999. Freetown ya sha wuta a waccar rana amma a yanzu muna cikin kwanciyar hankali".

11:45: Alkalin kotun ya ce masu gabatar da kara sun kasa bayyana cewa wanda ake zargin shi kadai ne ke da alhakin laifukan yakin da aka tafka a Sierra Leone.

11:42: Kotu ta fahimci cewa wanda ake zargi na da masaniya kan laifukan yakin da 'yan tawayen RUF suka aikata tun daga farkon watan Agustan 1997, lokacin da ya zama shugaban Liberia.

11:15: Ra'ayin Muzzammil Neatness shi ne: "Ya kamata a daina kiran kotun nan kotun duniya. Kamata yayi a kirata kotun yankewa 'yan Afrika hukunci. Ga manyan shugabannin duniya irin su Netanyahu na kasar Isra'ila nan, mai yasa baza su gurfanar dasu ba bisa laifin kashewa da murkushe Falasdinawa babu gaira babu dalili"?

10:50: Ra'ayin Abubakar Lawal Abubakar Daura shi ne: "Lallai wannan kotu idan ta zo kasa ta Najeriya za ta yi aiki ganin yadda ba a son hakkin bil'adama ba, kai Allah ya kai damo ga harawa".

10:45: A cewar Murtala M Jabbi: "Shi tsohon shugaban Amurka G W Bush, yafi karfin kotu ne duk irin ta'asar da ya tafka, amma duniya ta kama baki ta yi shuru"?

10:42: Ra'ayin Sade Saidu Daura kuwa shi ne: "To shugabannin Afrika, 'yan magana na cewa ganin buzu a masallaci ya ishi tinkiya wa'azi. Don haka shuwagabanni masu kama-karya sai ayi hattara.

10:40: A sakon da ya rubuta a shafin BBC Hausa Facebook Abdullateef Tanko Nayashi cewa yayi: "Jinin yara da mata da aka yiwa fyade a lokacin yakin Laberiya ba za su tafi a banza ba. Allah zai sa ka musu".

10:36: Alkalin kotun ya ce masu gabatar da kara sun gamsu cewa kungiyar 'yan tawaye ta RUF ita ce da alhakin kisa, da fyade da yanke sassan jikin mutane lokacin yakin basasar Sierra Leone, sai dai har yanzu bai ce ko Mr Taylor na da alaka da wadannan laifuka ba.

10:30: Alkalin kotun ya ce sun samu shaidun cewa an sace dukiyoyin jama'ar da basu-ji-basu-gani ba tare da farfasa bankuna domin sace kudaden ciki, laifin da ya sabawa dokokin kotun duniya. Kuma duka an aikata hakan ne domin a samu damar aikata ayyukan ta'addanci da rura wutar rikici a kasar Sierra Leone.

10:27: An tilastwa kananan yara da fararen hula shiga cikin harkokin soji sakamakon sace su da aka rinka yi a kasashen Sierra Leone da kuma Liberia.

10:24: Kimanin mutane 50,000 ne aka kashe a yakin na kasar Sierra Leone sannan wasu dubbai aka sassare musu sassan jikinsu, laifin da aka dora kan 'yan tawayen da ke goyon bayan Charles Taylor.

10:18: Idan aka same shi da laifi, zai zamo tsohon shugaban kasa na farko da kotun duniya ta samu da laifi kan aikata laifukan yaki tun bayan shari'ar Nuremburg biyo bayan yakin duniya na biyu.

10:09: Zargin da ake yi masa ya shafi mummunan yakin basasar da aka tafka ne a makwafciyar kasarsa ta Sierra Leone, ba wai rikicin kasar ta Liberia ba.

10:05: Ana yi masa shari'a ne a wata kotu ta musamman da Majalisar Dinkin Duniya ke marawa baya kan rikicin da aka tafka a kasar Sierra Leone wacce ke zama a birnin Hague na kasar Holland.

10:01: Ana tuhumar tsohon shugaban Liberia Charles Taylor ne da aikata laifukan yaki guda goma sha daya da kuma cin zarafin bil'adama, abinda kuma ya musanta.

09:57: A sakon da Abubakar Kalajanga Jalingo ya aiko a shafinmu na BBC Hausa Facebook, ya ce "da fatan wannan shari'a za ta zamo darasi ga azzaluman shugabanin kasashen mu na Afrika ma su ci da gumin talakawa".

09:27: Ana saran alkalan kotun duniya za su yanke hukunci kan shari'ar da ake yiwa tsohon shugaban kasar Liberia Charles Taylor bisa zargin aikata laifukan yaki bayan shafe shekaru biyar ana gudanar da shari'ar.

Karin bayani