Yaro daya na mutuwa a minti daya kan cizon sauro

Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption cizon sauro

Yau ce ranar zazzabin cizon sauro ta Duniya, ana kuma bikin tunawa da wannan rana a yau.

Hukumar lafiya ta duniya dai na kira da a fito da sabbabin matakai na kwajin cutar da kuma maganinta, cutar da har yanzu take kashe daruruwan dubban rayuka a duk shekara, galibinsu kananan yara.

A wata sanarwa daga Hedikwatar- ta dake Geneva, Hukumar lafiya ta duniya tayi gargadin cewa sakar- jiki da kuma rage kudaden da ake kashewa wajen yakar zazzabin cizon sauro, yana zama wani hadari da yake dakile cigaban da aka samu wajan yakar cutar, fiye da shekaru goma da suka wuce.

Karin bayani