'Dalilan kai wa This Day hari'

Ofishin jaridar This Day
Image caption Ofishin jaridar This Day

Wata jaridar da ke yada labaranta ta hanyar internet, watau Premium Times, tace kungiyar Boko Haram ta shaida mata dalilan da suka sa ta kaiwa gidan jaridar This Day dake Abuja da kuma Kaduna hari a jiya.

Kimanin mutane bakwai ne aka ce sun rasa rayukansu a hare haren.

A cewar Premium Times, kungiyar Boko Haram ta ce ta dau matakin ne, saboda kafafen yada labarai na danganta ta da wasu abubuwan da basu shafe ta ba, wadanda kuma ba 'ya'yanta ba ne suka aikata.

Kungiyar tayi barazanar cigaba da kaiwa kafafen yada labaran da ta ce basa mata adalci hare haren.

Karin bayani