ECOWAS za ta tura soji zuwa Mali da Guinea-Bissau

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugabannin ECOWAS a lokacin da suke gudanar da wani taro

Wani taron gaggawa da ECOWAS ta gudanar ya yanke shawarar tura dakarun yankin zuwa kasashen Guinea Bissau da Mali domin sa ido ga mayar da kasashen ga mulkin farar hula bayan juyin mulkin da sojoji suka yi kwanakin baya a kasashen.

Shugabannin kungiyar ta ECOWAS sun ce za a tura sojoji kimanin dari shida zuwa Guinea-Bissau.

Sun kuma baiwa gwamnatin mulkin sojin kasar sa'oi saba'in da biyu ta kiyaye da wannan umurni, ko kuma a sanya mata takunkumi.

A Mali kuma, za a tura sojoji dubu uku don taimaka wa gwamnatin rikon-kwarya kwato yankin arewacin kasar da ke hannun 'yan tawaye.

Kungiyar ta ECOWAS ta baiwa kasashen wa'adin watanni goma sha biyu na komawa ga mulkin farar hula, kuma cikin wannan lokacin ne za a shirya zabe.

Karin bayani