'Yan kasar Saliyo sun yaba kan shari'ar da aka yi wa Charles Taylor

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Charles Taylor

Mutanen da 'yan tawaye suka gallaza wa a yakin basasar da aka yi a kasar Saliyo sun yi marhabin da tuhumar da aka yi wa tsohon shugaban Liberia, Charles Taylor.

Wata kotu ta musamman ce dai ta samu Mr Taylor da laifin goyon bayan rura wutar rikici da cin zafarin da 'yan tawaye suka yi wa jama'a a kasar ta Saliyo.

Mutane da dama da ko dai aka sare wa wani sashe na jiki ko kuma suka rasa 'yan uwansu sun ce suna ganin an yi adalci a shariar.

Abdel wani dan jarida dan kasar Saliyo da ke aiki da BBC ya ce ya gamsu da hukuncin da aka yanke wa Charles Taylor:

"Na yi farin ciki saboda ganin cewa Charles Taylor ya fuskanci shari'a. An samu wanda ya tallafa aka kashe kakana da laifi''.

Karin bayani