An kashe mutane uku a jahar Adamawa

An kashe mutane a Adamawa Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An kashe mutane a Adamawa

Rahotanni daga jahar Adamawa a Najeriya na cewa an kashe akalla mutane uku a hare haran da aka kai a daran jiya a Yola babban birnin jahar.

A hari na farko wasu 'yan bindiga ne suka kashe mutane biyu a Jimeta, ya yin da 'yan sanda kuma suka kashe wani dan bindiga a wata aragamar da sukai da 'yan bindigar a kan hanyar da ta hade Jimetan da Yola.

Yanzu haka kuma jama'a a jahar ta Adamawa dai na ta nuna damuwarsu game da halin rashin tsaron da suka ce ana ciki a jahar.

A wani labarin kuma kungiyar tuntuba ta dattwan arewacin Najeriya ta nuna damuwa a bisa rashin kwanciyar hankalin da ake ci gaba da samu a arewacin kasar, musamman tashe tashen bama bamai da kuma hare hare, inda ta nuna mamaki matuka a bisa harin da aka kai a offisoshin wasu gidajen jaridu a abuja da kuma kaduna.

Karin bayani