Ashton na ziyara a kasar Burma

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Catherine Ashton

Babbar jami'a mai kula da harkokin waje a Tarayyar Turai Catherine Ashton ta sauka kasar Burma don nuna goyon bayan Tarayyar Turai ga sauye-sauyen siyasar da aka samu kwanan nan a kasar.

Ms Ashton za ta gana da ministocin gwamnati da jagorar 'yan adawa, Aung San Suu Kyi.

Haka kuma za ta bude wani sabon ofishin jakadanci na Tarayyar Turai.

Tarayyar Turan ta janye takunkumin da ta garkamawa kasar Burma tun farkon wannan watan, to amma ta ce tana son ganin an samu karin ci gaba ta fuskar kafa dimokaradiyya kafin janye takunkumin baki dayan sa.

Karin bayani