Shugabar Liberiya da ta Malawi na ganawa

Shugabar kasar Liberia Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugabar kasar Liberia

Shugabannin Afirka biyu mata na ganawa a yau, inda shugabar Liberia, Ellen Johnson Sirleaf, za ta shirya liyafar cin abincin dare, domin karrama sabuwar shugabar kasar Malawi, Joyce Banda.

Mrs Banda ta bayyana takwarar tata ta Liberia da cewa, abar koyi ce a gareta.

Ta ce, tana fatan gano sirrinta, a lokacin ziyarar da ta kai mata.

A nata gefen, shugaba Ellen Johnson Sirleaf ta bukaci Joyce Banda da kada tayi sako-sako wajen jaddada ikonta a Malawi.

Mrs Sirleaf ta yi marhabun da rantsar da Joyce Banda a matsayin shugabar kasar Malawi, a farkon wannan watan da muke ciki. Ta ce, a yanzu kam bata jin kadaici.

Karin bayani