Saudiyya ta rufe ofisoshin jakadancinta a Masar

Zanga zangar neman Saudiyya ta sako Ahmed El-Gizawy Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Zanga zangar neman Saudiyya ta sako Ahmed El-Gizawy

Saudiyya ta kira jakadanta da ke kasar Masar, kuma ta rufe dukan ofisoshin jakadancinta a Masar din, bayan munanan zanga zangar da aka yi, na yin Allah wadai da kamun da hukumomin Saudiyyar suka yiwa wani lauya dan kasar Masar, mai fafutukar kare hakkin jama'a.

A farkon wannan watan ne mahukuntan Saudi Arabiyar suka kama Ahmed El-Gizawy, yayin da ya je Umara, saboda a cewarsu, yayi kokarin shiga da wasu abubuwan da aka haramta cikin kasar.

To sai dai 'yan gwagwarmaya sun yi imanin cewa, kamun Ahmed El-Gizawyn, yana da alaka da wata karar da ya shigar kotu, kan yadda ake kuntatawa fursunoni 'yan kasar Masar a Saudiyya.

A farkon wannan watan, daruruwan mutane sun yi zanga zanga a gaban ofishin jakadancin Saudiyya a birnin Alkahira, suna neman a sako lauyan ba tare da bata lokaci ba.