Soji sun saki shugabanni a Guinea Bissau

Hakkin mallakar hoto
Image caption Raimundo Pereira

Manyan 'yan siyasar kasar Guinea Bissau su biyu, watau Carlos Gomez Junior da Raimundo Pereira, sun isa kasar Ivory Coast a karshen mako, inda za su gana da shugaba Allasane Outtara, bayan da sojin da suka yi juyin mulki a kasar a farkon watan da muke ciki, suka sake su.

Mr Gomez, shi ne kan gaba a zaben da aka gudanar a kasar, yayin da Mr Pereira kuma ke matsayin shugaban gwamnatin rikon kwarya gabanin juyin mulkin da sojin suka yi.

Mr Pereira ya shaidawa manema labarai jim kadan bayan da suka isa Ivory Coast, cewa sun je kasar ne domin godiya game da kokarin da kungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta yamma ECOWAS, wacce shugaban Ivory Coast din ke jagoranta, ke yi wajen ganin an dawo da kasar kan mulkin dimokaradiyya.

Sakin na su dai ya zo ne bayan matsin lambar da kungiyar ECOWAS ta yi wa kasar ne domin ta maida kasar kan turbar dimokaradiyya.

Tuni dai shugabannin mulkin sojin kasar suka amince da sharudan da kungiyar ta ECOWAS ta gindaya musu na shirya zabe da kuma mika mulki hannun farar hula cikin shekara guda.

Karin bayani