Zargin tallafawa 'yan tawayen Syria

'Yan adawa a Syria Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan adawa a Syria

Rundunar sojan ruwan kasar Lebanon ta kama wani jirgin ruwan da ke dauke da kwantena uku, makare da makamai da albarusai, wadanda mai yiwuwa za a kaiwa 'yan tawaye Syria ne.

A cewar rahotanni, jirgin ya taso ne daga kasar Libiya, sannan ya yada zango a Masar, kamin ya cigaba zuwa tashar jirgin ruwan Tripoli ta Lebanon.

Hukumomin Syria sun sha kokawa kan cewa, ana bi ta wannan tashar, wajen yin sumogal din makamai zuwa kasar.

Wakilin BBC a Lebanon ya ce, 'yan adawar Syria na da goyon baya sosai a Tripoli, kuma sabuwar gwamnatin Libiya na mara masu baya sosai.

Karin bayani