Gwamnatin Najeriya ta nemi tattaunawa da Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

Gwamnatin Najeriyar ta sake yin kira ga 'ya'yan kungiyar nan ta jama'atu Ahlus- sunna lidda'awati wal- jihad da aka fi sani da Boko Haram, da su fito a tattauna da su domin kawo karshen hare-haren da kungiyar take kaiwa.

Kiran na gwamnatin Najeriyar dai yazo ne kwanaki kalilan, bayan wasu hare-hare da aka kaddamar a kasar.

A wata ziyara da ya kai Jihar Gombe, mataimakin shugaban Najeriya, Architect Namadi Sambo ya yi kira ga kungiyar da ta fito a tattauna da ita domin samar da zaman lafiya a kasar.

"Ina kira ga wadannan mutane su fito a zauna da su domin an samu maslaha, ko shekaru hamsin aka yi ana yaki, dolene a zauna a teburin sulhu domin a samu maslaha." In ji Namadi Sambo.

Gwamnatin kasar dai ta nanata cewa za tayi iyakacin kokarinta domin tabbatar da tsaro a kasar inda mataimakin shugaban Najeriya, Namadi Sambo ya nemi al'ummar kasar da su taimakawa gwamnati kasar wajen tabbatar da tsaro a kasar.

"Zamu ci gaba da kokari, ganin cewa ko wani dan Najeriya a fadin kasar nan a ko ina ya samu isashen tsaron lafiya da kuma dukiyoyinsu.

"Muna kira da 'yan Najeriya su bada nasu gudunmuwar wajen taimaka gwamnati magance matsalolin tsaron dake addabar gwamnati kasar." In ji Namadi Sambo.

To sai dai kuma wasu na ganin cewar Gwamnatin Najeriyar bada gaske take ba, suna masu cewar ai gwamantin ta soma wannan tattaunawar da kungiyar a baya, daga baya kuma alamu suka bayyana cewa bada gaske gwamnatin take ba, don haka ma tattaunawar ta wargaje.