China ta baiwa Sudan Ta Kudu bashi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Sudan Ta Kudu Salva Kiir, da shugaban China, Hu Jintao

Sudan ta Kudu ta ce kasar China ta ba ta dala biliyan takwas a matsayin bashi don daukar nauyin ayyuka da dama na raya kasa cikin shekaru biyu masu zuwa.

Kudin sun ninka kasafin kudin shekara na Sudan ta Kudun.

Wani kakakin gwamnati a birnin Juba ya ce za a yi amfani da kudin ne wajen gina hanyoyi, da gadoji, da hanyoyin sadarwa.

Bai ambaci shirin shimfida bututun mai da zai ratsa tekun India ba.

Kasar China dai ita ce ke sayen mafi rinjayen man kasar Sudan; tana son ta ci gaba da kyakkyawan zumuncin da ke tsakaninsu da Sudan, dadaddiyar aminiyar ta da kuma Sudan ta Kudun, wadda a bara ta samu 'yancin kan ta.

Karin bayani