An kai hari a jami'ar Bayero dake Kano

Shugaban Najeria, Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaban Najeria, Goodluck Jonathan

A Najeriya, 'yan bindiga sun kai hari a jami'ar Bayero da ke Kano, inda suka hallaka akalla mutane goma sha bakwai.

Shaidu sun ce, mahara dayawa ne suka jefa bama-bamai, a wurin da Krista ke ibada a jami'ar Bayeron.

Daga nan kuma sai suka bude wuta a kan masu ibadar da ke kokarin tserewa daga wurin.

Wani kakakin 'yan sanda ya ce, mutane dayawa kuma sun ji munanan raunuka, kuma 'yan bindigar sun samu sun tsere a kan babura.

A watan Janairun da ya wuce, akalla mutane dari da tamanin da biyar ne suka rasa rayukansu, a lokacin hare-haren da kungiyar Boko Haram, mai gwagwarmayar Musulunci ta kai a Kanon.

Karin bayani