Sojin Mali sun yi watsi da shawarar ECOWAS

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Captain Amadou Sanogo

Shugaban sojin da suka yi juyin mulki a kasar Mali, Amadou Sanogo, ya ki amincewa da shawarar da kungiyar raya tattalin arzikin Afurka, ECOWAS ta yanke, ta aikewa da dakarunta cikin kasar domin su sanya ido kan yadda za a dawo da mulkin farar hula.

Captain Sanogo ya ce kungiyar ECOWAS din ba ta tuntube su game da batun ba kafin ta yanke shawara a taron da shugabannin ta suka gudanar a Abidjan.

Kazalika Captain Sanogo ya yi watsi da wa'adin da ECOWAS ta baiwa gwamnatin Mali domin ta dawo da mulkin farar hula cikin watannin goma sha biyu.

Ya ce bai kamata wata kungiya ta rika yin katsalandan cikin harkokin kasar ba.

Mayar da hannun agogo baya

Bayan da kungiyar ta ECOWAS ta sanyawa sojin takunkumi ne a farko watan Afrilu, sai suka maida iko hannun gwamnatin rikon kwarya, wacce shugaban majalisar dokokin kasar, Dioncounda Traore, ke jagoranta.

An dai rantsar da Mr Traore ne a matsayin shugaban kasar na wucin gadi, inda zai yi kwanaki arba'in, sannan a gudanar da zabe a karshen watan Mayu.

Don haka ne a cewar Captain Sanogo, ko bayan wadannan kwanaki arba'in sun shude, sojin ke da alhakin yadda za a ci gaba da matakin maida iko hannun fafaren hula, ba wai wata kungiya daga wajen kasar.

Wannan sa-toka-sa-katsi dai za ta jefa kasar cikin halin rashin tabbas a wannan lokaci da ake matukar bukatar zaman lafiya a cikinta.

Karin bayani