'Yan gudun hijira daga Mali na karuwa a Niger

'Yan gudun hijirar Mali a Niger Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan gudun hijirar Mali a Niger

Rahotanni daga jahar Tilaberi a janhuriyar Nijar na cewa har yanzu jama'a daga kasar Mali na ci gaba da yin gudun hijira zuwa kasar ta Nijar.

Kungiyoyin bada agaji sun ce rikicin 'yan tawaye a arewacin Mali hadi da matsalar karancin abinci ne ke tilastawa daruruwan mutane yin gudun hijra daga kasar ta Mali.

Duk da cewa Najir na daga cikin kashen da ke fuskantar matsalar karancin cimaka, amma dai gwamnatin kasar tare da wasu kungiyoyin kasashen waje na ta kokarin tallafawa 'yan gudun hijirar da yanzu haka ke zaune a sansanoni daban daban a duk fadin kasar.

Kungiyar World Vision International na daga cikin kungiyoyin dake tallafawa 'yan gudun hijirar na Mali, kuma a kwannan sun ziyarci sansanin 'yan gudun hijirar dake Mangaize a gundumar Walam dake jahar Tilaberi.

Suwaiba Ahmad ta tuntubi Malam Amadou Baraje Nakaka na kungiyar ta World Vision International domin jin karin bayani kan abin da suka gani a wajen.

Karin bayani