Sudan ta ba dubban jama'a wa'adin su koma Sudan ta Kudu

Shugaban Sudan Omar al-Bashir Hakkin mallakar hoto q
Image caption Shugaban Sudan Omar al-Bashir

Kasar Sudan ta bukaci wata kungiyar kabilu 'yan kasar Sudan ta kudu su dubu goma sha biyu da su fice daga kasar nan da mako guda.

Kungiyar Kabilun dai sun tare ne a garin Kotsi da ke kan iyaka a 'yan makwannin da suka gabata, bayan sa gwamnati Sudan ta umarci 'yan kasar Sudan ta kudu dake zaune a arewacin kasar da su fice daga kasar, ko kuma su sabunta takardun zama 'yan kasa.

A yayinda ake ci gaba da zaman dar-dar tsakanin kasar Sudan da Sudan ta kudu, har yanzu ana ci gaba da fafatawa a kan iya kokin kasashen biyu, kuma sama da 'yan kasar Sudan ta kudu dubu dari uku da hamsin ne da ke zaune a arewacin Sudan KE cikin halin kakanikayi.

Yawancinsu su koma arewacin Sudan ne a shekara ta 2002 domin neman aikin bayan an kulla yarjejeniyar zaman lafiya.

Amma a bana gwamnatin Sudan ta kudu ta sanya wa'adin ranar takwas ga watan Afrailu ga duk kabilun 'yan kasar Sudan ta kudu dake zaune a Sudan din da su sabonta takardun zaman 'yan kasa kuma su bar kasar.

Dubban 'yan kasar Sudan ta kudu dake kaura zuwa kudancin Sudan sun kakare a wani tashar ruwa dake garin Kotsi dake kan iyaka da kasar Sudan ta kudu. Gwamnan garin dai ya nemi su da su tattara yanasu yanasu su watse saboda fargabar tsaro a yayinda ya basu mako guda da su bar garin.

Amma gwamnatin Sudan ta ki barin jiragen ruwa su shigo daga Sudan ta kudu domin su kwashe 'yan gudun hijira.

Gwamnatin Sudan dai tana neman Sudan ta kudu da ta bata tabbacin cewa ba za'a yi amfani da jiragen ruwan wajen shigowa da makamai ba ko kuma mayaka zuwa arewacin kasar ba.

Karin bayani