Mutane tara sun hallaka a Zamfara

Image caption Wata mota da ta yi hatsari a Najeriya

Akalla mutane tara ne suka mutu a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya bayan da motar da suke ciki ta yi hatsari.

Haka kuma wasu mutanen kimanin 33 sun samu raunuka.

Motar, kirar akori-kura ta kife ne da safiyar ranar Lahadi a kusa da garin Mafara na jahar Zamfara.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadurra a jahar ta Zamfara, Muhammed Garba, ya shaidawa BBC cewa da alama barci ne ya kwashe direban motar, wadda ta dauko mutane 45 yawancinsu 'yan ci-rani tare da kayyakkinsu.

Mutanen suna kan hanyar su ne ta komawa gida daga birnin Minna na jahar Naija zuwa Sakkwato.

Karin bayani