An wayi gari da karar harbe-harbe a Kano

Hakkin mallakar hoto 1

Rahotanin d daga jihar Kano a arewacin Najeriya na cewa an wayi gari da jin karar harbe-harben bindigogi a jihar.

An dai ji karar harbe-harben ne a yankin sharada da kuma Sabuwar gandu dake cikin birnin tun daga musalin karfe hudu na asubahin har zuwa karfe shida na safiya.

Rudunar tsaro ta JTF ta shaidawa BBC cewa ita ce ta kai samame a wani mabuyar 'yan bindiga.

Amma ya zuwa yanzu ba ta bada karin haske game da samamen da ta kai ba.

A yanzu haka dai rahotannin na cewar komai ya lafa a yanzu.