An fafata a Mali tsakanin sojoji

Hakkin mallakar hoto AFP

A kasar Mali, Sojojin da ke gadin fadar Shugaban kasa da kuma wadanda biyayya ga shugabanin da su ka yi juyin mulki a watan Mayu din da ya gabata sun yi musayar wuta.

Wani mai magana da shugabanin a su ka yi juyin mulkin ya ce Sojojin da ke kusa da tsohon shugaba Amadou Toumani Tooure da aka habbarar na kokarin yin wani juyin mulkin.

Rahotanni dai sun ce ana ta jin karar harbe-harbe a filin jiragen sama da kuma kuma kafar yadda labarai na kasar.

An dai fara fadan ne a yammacin jiya a lokacin da sojojin da kekusa da tsohon shugaban kasa, Amadou Toumani Toure su ka yi kokarin kwace kafar yadda labarai na kasar daga sojojin da su ka yi juyin mulki a watan mayun da ya gabata.

Shugabanin da su ka yi juyin mulkin dai sun ce, sojojin sojojin da ke kusa da tsohon shugaban kasar har wa yau sun yi kokarin kwace filin sauka da tashin jiragen saman kasar domin shirin zuwan sojoji daga kasashen yammacin Afrika da za su taimakawa kasar wajen dawowa da ita kan tafarkin demokradiyya, yunkurin da kuma a kwanann shugabanin da su ka yi juyin mulki su ka yi watsi da shi.

Wadanda su ka gani da ido sunce tituna a Bamako fayau su ke a yayinda kuma babu wutan lantarki a yawancin fadin jihar.

Gidan talbijin din jihar dai na ta maimaita shirye-shirye na musamman ne a maimakon,labaran da aka saba yadawa.