An kashe mutane 20 a kasar Masar

An kashe mutane 11 a kasar asar Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga-zangar na goyon bayan wani dan takarar shugaban kasa ne da aka haramta wa takarar

Akalla mutane 20 aka kashe a kasar Masar lokacin da aka kai hari kan masu zanga-zangar nuna adawa da shugabannin mulkin sojin kasar.

Wasu mutane ne dauke da miyagun makamai da suka hada da bindigogi da kulake da kuma bama-bamai hadin- gida, suka farma mutanen a kofar ma'aikatar tsaron kasar.

Sama da mutane 100 ne kuma suka samu raunuka a harin.

Wakilin BBC a birnin Alkahira ya ce, wasu rahotanni na cewa maharan mazauna yankin ne, wadanda suka husata da yadda masu zanga zangar ke kawo musu cikas a harkokin kasuwancinsu.

Sai dai 'yan kasar ta Masar da dama na cewa ko ba komai, gwamnati ta kawar da kai ga abin da ya farun.

An kai wa masu zanga-zangar hari ne da asubahi, a inda suka kafa sansani a wajen ma'aikatar tsaron.

Suna adawa ne da cire sunan Hazem Abu Ismail, wani mai kaifin ra'ayin Islama, daga jerin 'yan takarar shugaban kasa, a zaben da za a gudanar a wannan wata.

Karin bayani