Babu na zabe tsakanin Sarkozy da Hollande - Le Pen

le pen Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Marine Le Pen

Shugabar jam'iyyar masu matsanancin ra'ayin rikau ta Faransa, Marine Le Pen ta ki amincewa ta mara baya ga kowane, daga cikin 'yan takarar shugaban kasar zagaye na biyu da za a gudanar ranar Lahadi.

A cewar Le Pen za ta kada kuri'arta ce ba tare da zaben kowa ba, ta kuma yi kira ga magoya bayanta da su zabi abin da ransu ya raya masu.

Marine Le Pen ta kara da cewar 'yan takarar biyu wato shugaba Sarkozy da abokin hamayyarsa, na jam'iyyar gurguzu Francois Hollande zasu mika ragamar ikon kasar ne ga tarayyar Turai.

Mutane miliyan shidda da suka kada wa Mis Le Pen kuri'a a zagayen farko na zaben shugaban kasar, kuma su ake ganin zasu iya raba gardama a zaben zagaye na biyu.

Mista Sarkozy na ta fadi tashi ne na ganin ya samu goyon bayansu, inda a yau yake furta cewar, yawan baki a Faransa ya zarta kima.

Karin bayani