'Murdock bai cancanci shugabanci ba'

Rupert Murdoch Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rupert Murdoch

Sakamakon wani bincike da wani kwamitin majalisar dokokin Birtaniya ya gudanar ya yanke shawarar cewa Rupert Murdoch, daya daga cikin masu kafafen yada labaran da suka fi fada-a-ji a duniya, bai cancanci ya jagoranci katafaren kamfanin ba.

A cikin rahoton da aka dade ana jiran fitarsa, kan abin kunyar nan da ya shafi satar sauraro ko karanta sakonnni a wayoyin jama'a, a daya daga ciki jaridunsa, kwamitin ya zarge shi da kawar da kai da gangan daga abubuwan dake faruwa a katafaren kampanin nasa na kafafen yada labarai.

Sai dai kuma da dama daga cikin 'yan kwamitin sun ki su goyi bayan kakkausar sukar da aka yi wa Mr Murdoch.

Ana zargin kamfaninsa na Birtaniya, News International cewar bai gayawa majalisar dokoki gaskiya ba akan batun satar sauraro ko karanta sakonnni a wayoyin jama'a.

Manema labarai a tsohuwar jaridar ta News of the World suna satar shiga wayoyin shahararrun mutane da 'yan siyasa harma da na miyagun mutane.

Karin bayani