Aung San Suu Kyi ta soma aiki a majalisar dokoki

Aung San Suu Kyi na shan rantsuwar kama aikin majalisar dokoki Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jam'iyyar Aung San Suu Kyi ta yi nasara a zaben cike- gurbin da aka gudanar

Jagorar tabbatar da demokradiyya a Burma , Aung San Suu Kyi, wacce ta shafe kusan shekaru ashirin karkashin daurin talala, bayan tayi adawa da mulkin sojoji, a yanzu ta soma aiki a matsayin 'yan majalisar dokoki

Ta dai sha rantsuwar kama aiki wata guda bayan nasarar data samu tare da jam'iyyarta a zaben cike- gurbin da aka gudanar

A baya dai, ta nuna cewar bata amince da kalaman da ake amfani dasu wajen shan- rantsuwar kama aikin ba

Sai dai a yanzu Aung San Suu Kyi ta yanke shawarar canza matsayinta, darajar al'ummar Kasar Burma

Karin bayani