BBC navigation

Aung San Suu Kyi ta soma aiki a majalisar dokoki

An sabunta: 2 ga Mayu, 2012 - An wallafa a 07:23 GMT
Aung San Suu Kyi na shan rantsuwar kama aikin majalisar dokoki

Jam'iyyar Aung San Suu Kyi ta yi nasara a zaben cike- gurbin da aka gudanar

Jagorar tabbatar da demokradiyya a Burma , Aung San Suu Kyi, wacce ta shafe kusan shekaru ashirin karkashin daurin talala, bayan tayi adawa da mulkin sojoji, a yanzu ta soma aiki a matsayin 'yan majalisar dokoki

Ta dai sha rantsuwar kama aiki wata guda bayan nasarar data samu tare da jam'iyyarta a zaben cike- gurbin da aka gudanar

A baya dai, ta nuna cewar bata amince da kalaman da ake amfani dasu wajen shan- rantsuwar kama aikin ba

Sai dai a yanzu Aung San Suu Kyi ta yanke shawarar canza matsayinta, darajar al'ummar Kasar Burma

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.