Bolivia ta kwace kamfanin wutar lantarki na Spain

Evo Morales na Bolivia Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Evo Morales na Bolivia ya kwace kamfanin wutar lantarki na Spain

Shugaban Bolivia Evo Morales ya maida wani kamfanin samar da hasken wutar lantarki na Spain mallakar gwamnatinsa

Mr. Morales ya baiwa sojoji umarni su karbe ragamar kamfanin na REE, wanda yake gudanar da kashi uku bisa hudun hasken wutar lantarkin Bolivian

Wakilin BBC Yace shugabanKasar ya kare matsayin daya dauka, yana mai cewa Kamfanin, bai zuba isashen jarin da- ake bukata ba a Bolivian, cikin shekaru goma sha- shidan da yayi yana harka a cikin Kasar

Sai dai jakadan Kasar Spain a Bolivia Ramon Santos, yace karbe ragamar kamfanin ya haifar da rashin yarda