Chen ya bar ofishin jakadancin Amurka a Beijing

chen Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Chen Guangchen a asibiti

Mai bijire wa gwamnatin kasar Chinar nan, Chen Guangchen ya ce ya bar ofishin jakadancin Amurka dake birnin Beijing, inda ya nemi mafaka, bayan da ya ce yana fargaba game da tsaron lafiyar Iyalinsa.

An ambaci Mr Chen yana cewa an shaida masa cewar za a kashe matarsa, idan ya ci gaba da zama, kuma wani jami'in gwamnatin Amurka ne ya sanar da shi hakan.

Li Jinsong, wani lauya ne kuma aboki ga Mr Chen "lokacin da Chen ya yi magan da ni, ya ce ne ya bar ofishin jakadancin, kuma yana kan hanyarsa ta zuwa asibitin Chaoyang".

Sai dai Amurka na cewa babu wani jami'inta da ya yi magana da Mr Chen kan barazanar Chinar, kuma ya bar ofishin jakadancin ne bisa radin kansa, bayan an ba shi tabbacin kare lafiyarsa.

China dai na zargin Amurka da yi ma ta katsalandan a harkokinta.

Karin bayani