Za a baiwa 'yan jarida kariya a Najeriya

ig Hakkin mallakar hoto Aliyu
Image caption Speto Janar Muhammed Abubakar

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bada umurnin baiwa ofisoshin kafafen yada labarai kariya ta musamman.

Wannan umurni na zuwa ne bayan da aka kai hari a ofishin jaridar Thisday, tare da barazanar da kungiyar Jamaatu Ahlissuna Lidda'awati wal Jihad da aka fi sani da suna Boko Haram ta yi ga wasu kafafen yada labarai.

Hukumar 'yan sandan ta ce, kariyar ta danganta ne da bukatar kafar yada labaran.

Sanarwar hakan ta fito ne daga babban sifeton 'yan sanda kasar Muhammad Abubakar, wanda ya umurci dukkanin kwamishinonin 'yan sandan kasar da aiwatar da umurnin.

To sai dai abin dubawa a nan shi ne, anya wannan kariyar ba za ta kara fallasa ofisoshin yada labarun ba, amma kakakin 'yan sandan kasar, Frank Mba ya ce "babban sifeton yan sandan ya ce, matakin ya dogara ne ga kafofin yada labarun, idan ba sa so, ko kuma su na gani zai fallasa su, akwai hanyar ba su kariya wadda bai kamata a bayyana ta a fili ba".

Rundunar 'yan sandan dai ta ce, wannan mataki ba wai ta dauke shi ne da nufin haddasa rudu a tsakanin kafafen yada labaru ba, illa kwantar ma su da hankali, wanda zai ba su damar gudanar da aiyukan su kamar yadda ya kamata.

Matakin na zuwa ne bayan da kungiyar Jamaatu Ahlissuna Liddaawati wal Jihad da aka fi sani da suna Boko Haram ta yi barazana ga wasu kafafen yada labaru na kai masu hare hare, yayinda a bagare guda kuma matsalar tsaro a kasar ke kara ta'azara.

Karin bayani