Ga alama gwamnatin Sin tana tsare ne da Chen a asibiti

Amurka ta ce makahonan dan China, Chen Guangchen da yake bijirewa kasar sa, ya amince zai bar kasar, a wani lamari da ya kankane tattaunawar da kasashen biyu keyi.   A gabanin fara wata tattaunawa da mahukuntan China, a Beijing, Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton, tayi hannunka mai sanda ga Chinar akan maganar Mista Chen, koda yake bata ambace shi kai tsaye ba  Misis Clinton tace "ai kamar yadda Shugaba Obama ya fada ne a makon jiya, idan kasar China ta mutunta 'yan cin dukkan 'yan kasar ta, karfin tattalin azrkin ta zai karu, kuma hakan zai sa dangantarkar mu ta kara karfi".  Mista Chen ya ce yana so ya tattauna da jami'an Amurka akan shawara sa ta barin kasar amma kuma yana ganin kamar an hana su ganawa da shi a sibitin da yake a Biejing.
Image caption Chen Guangchen

Da alama makahon nan dan kasar Sin dake fafutukar kare hakkin dan adam yayin da ake tsakiyar wata takaddamar diplomasiyya tsakanin Beijing da Washington, yana tsare a asibiti - kwana daya bayan tabbacin da mahukuntan Chinan suka ba shi na kare lafiyarsa da 'yancin walwala.

Mr Chen ya shaida wa BBC cewa an hana jami'an diplomasdiyyar Amurka ganinsa a asibiti.

Ya ce China ta karya yarjejeniyar da aka cimma jiya-jiyan nan, wadda a karkashinta ne ya amince ya bar ofishin jakadancin Amurka inda ya samu mafaka kwanaki shiddan da suka wuce.

Ya roki sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton da ta taimake shi da iyalinsa su bar China.

Karin bayani