An bayyana farashin hannayen jarin Facebook

An bayyana farashin hannayen jarin Facebook Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kimanin mutane miliyan 900 ne ke amfani da Facebook a duniya

Kamfanin sada zumunta na facebook ya bayyana farashin hannayen jarinsa da zai fara sayarwa ga jama’a.

Farashin zai kama ne daga dala 28 zuwa dala 35, wanda zai sa darajar kamfanin ta kai kimanin dala biliyan 85 zuwa 95.

Sayar da hannayen jarin shi ne mafi girma da wani kamfanin internet ya yi a tarihi, tun na kamfanin Google – wanda ya sa darajar Google din ta kai dala biliyan 23 a shekara ta 2004.

Za a fara sayar da hannayen jarin kamfanin Facebook a kasuwar hannayen jarin Amurka ta Nasdaq, inda zai yi gogayya tare da abokan hamayyarsa na Amazon da Cisco.

Ana saran Facebook zai fara tallata hannayen jarin na sa ranar Litinin, kafin a fara sayar dasu a ranar 18 ga wannan watan.

Sai dai fiye da kashi goma cikin dari na kamfanin ne kawai za a sayar, wanda ake saran zai samar da dala biliyan 12 ga kamfanin.M

Masana na dari-dari

Shafin Facebook wanda aka kafa shekaru takwas da suka gabata, yana da mutane miliyan 900 da ke amfani da shi a duniya.

Ko a bara ribar dala biliyan daya kamfanin ya samu.

Sai dai masu lura da al’amura na dari-dari da makomar kamfanin a nan gaba, ganin yadda a makon da ya gabata, ya bada rahoton samun koma-baya a kudaden shigarsa a karon farko.

Sai dai a wani jawabi da shugaban kamfanin Mark Zurkeberg, ya yi, ya ce suna maida hankali ne wurin shawo kan wannan fargabar, ta hanyar zuba jari a fannin wayar salula saboda bunkasar da fannin ke kara yi.

Mark Zurkeberg zai ci gaba da kasancewa shugaban kamfanin bayan an sayar da hannayen jarin, inda yake da kashi 57 cikin dari na kuri’a saboda hannayen jarin da ya mallaka da kuma yarjejeniyar daya cimma da sauran masu hannun jari a kamfanin.

Zai mallaki kashi 31 cikin dari na hannun jari, wanda zai kai adadin abinda ya mallaka zuwa sama da dala biliyan 17.

Wanann adadi ka iya sa shi ya zamo na 33 a jerin mutanen da suka fi kudi a duniya da jaridar Forbes ta ke wallafawa.

Karin bayani