Ya kamata a sasanta tsakanin China da Amurka -Clinton

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Chen Guancheng

Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka, Hillary Clinton, wacce ke ziyarar aiki a Beijing, ta ce Amurka da China na da dangantaka ta keke-da-keke, wadda za ta ba su damar tattauna bambance-bambancen da ke tsakaninsu.

Ta furta wadannan kalamai ne a daidai lokacin da ta da jijiyoyin wuya ke karuwa tsakanin kasashen dangane da halin da mai fafutukar kare hakkin bil Adaman nan Chen Guangcheng ke ciki.

Ranar Alhamis Mista Chen ya mika koke na ba-zata kai tsaye ta waya ga Majalisar Dokokin Amurka.

Chen ya ce yana so ne ya je Amurka don ya huta, kuma yana fatan samun taimakon Sakatariyar Harkokin Wajen, Hillary Clinton.

Ga alama Mista Chen na tsare ne a wani asibiti duk kuwa da sharuddan da hukumomin China suka bayar da tabbacin za su cika kafin barinsa ofishin jakadancin Amurka ranar Laraba.

'Yan sanda da dama ne dai suka yiwa ginin asibitin kawanya, kuma Mista Chen ya shaidawa BBC cewa ana hana jami'an diflomasiyyar Amurka kai masa ziyara.

Kasar China dai ta ce Mr Chen na da damar zuwa kasashen waje domin zurfafa karatunsa na jami'a.

Karin bayani