Musulmi sun yi wa shugaban Kiristoci raddi

Image caption Pastor Ayo Orisejafor

Kungiyar Jama'atu Nasril Islam a Najeriya ta bayyana damuwarta dangane da kalaman da shugaban kungiyar Kiristocin kasar, Pastor Ayo Orisejafor, ya yi cewa a kan Kiristocin kasar aka fi kaddamar da hare-hare.

A wata ganawa da manema labarai a Kaduna, kungiyar ta Jamaatu Nasril Islam ta bayyana kalaman shugaban kungiyar ta CAN da cewa barazana ce ga gwamnati da kuma musulmi.

Babban sakataren kungiyar, Sheikh Dokta Khalid Aliyu Abubakar, ya ce su ma musulmi sun fuskanci hare-hare amma gwamnati ba ta dauki wani mataki ba:

''Mun yi bayanin abin da ya faru na karamar sallar da aka yi a Jos, aka kashe musulmi; suka sanar amma gwamnati ba ta yi komai ba. Kuma kowa ya ji ya gani.Wa muka yi wa barazana a kasar nan? Abin da aka yi a Kudancin Kaduna; aka dinga yanka musulmi; wa muka yi wa barazana?''

Sheikh Abubakar ya ce yana goyon bayan tattaunawa da masu tayar da kayar baya domin magance matsalolin da ke addabar kasar.

Karin bayani